Isa ga babban shafi
Yemen

Dawo da zaman lafiya a Yemen

Manzon Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin Yemen Martin Griffiths, ya gana da jagoran ‘yan tawayen Huthi inda ya gabatar masa da daftarin da ke kunshe da batutuwan da ake shirin tattaunawa don samar da zaman lafiya a kasar cikin watan disemba mai zuwa.

Martin Griffiths mai shiga tsakani a rikicin Yemen
Martin Griffiths mai shiga tsakani a rikicin Yemen REUTERS/Tarek Fahmy/File Photo
Talla

Martin Griffiths, wanda ya isa birnin Sana’a tun ranar larabar da ta gabata, na kokarin shawo kan bangaren gwamnati da na ‘yan tawayen Huthi ne domin amincewa da shiga tattaunawar samar da zaman lafiya da za a fara a farkon watan gobe a kasar Sweden.

A yau juma’a babban jami’in diflomasiyar zai ziyarci garin Hodeida mai tashar jiragen ruwa, inda aka share tsawon watanni ana gwabaza fada tsakanin bangarorin biyu, tare da jefa milyoyn mutane a cikin mummunan yanayi na yunwa a kasar ta Yemen.

Rikici a Yemen ya kara tsakananta ne, bayan da rundunar hadin-gwiwa karkashin jagorancin Saudiya ta kaddamar da farmaki a kan ‘yan tawayen Huthi da ke samun goyon bayan kasar Iran.

Ko baya ga mutuwar dubban mutane, Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane milyan 14 ne ke fama da yunwa a kasar,yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke fatan ganin an kawo karshen wannan yaki ta hanyar shirya wannan taro na tattaunawa a birnin Stockholm na kasar Sweden, a farkon watan gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.