Isa ga babban shafi
Amurka-Africa

Amurka ta nemi kawo karshen ayyukan wanzar da zaman lafiya a Afrika

Amurka za ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta kawo karshen ayyukan wanzar da zaman lafiya musamman ayyukan da aka fahimci cewa ba za su iya samar da zaman lafiya a gaggauce ba.

Mai bai wa shugaba Donald Trump shawara kan sha’anin tsaro John Bolton.
Mai bai wa shugaba Donald Trump shawara kan sha’anin tsaro John Bolton. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Mai bai wa shugaba Donald Trump shawara kan sha’anin tsaro John Bolton da ke gabatar da jawabi a cibiyar Heritage Foundation, ya ce babbar manufar Amurka ita ce kawo karshen rikicin amma ba kwantar da shi na dan gajeren lokaci ba.

Jami’in ya zana kasashe irinsu Sudan ta kudu da suka kasa cimma manufa ta gari duk da irin taimakon da Amurka ke bayar zuwa ga sha’anin tsaro.

Acewar Amurka ba dai dai ba ne a rika bata kudi da lokaci wajen yunkurin sasanta rikicin kasashen na Afrika musamman wadanda aka san baza su taba sasantawa ba sai dai rikicin ya dan lafa zuwa wani lokaci kuma ya ci gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.