rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Tarayyar Turai Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana zargin Ronaldo da fyade a Las Vegas na Amurka

media
Cristiano Ronaldo dan wasan Fotugal REUTERS/Massimo Pinca

Yan Sanda birnin Las Vegas na kasar Amurka na daf da bayar da samacin a kamo musu dan wasan kasar Fotugal Cristiano Ronaldo.

Ana zargin wannan dan wasa da aikata fyade sama Kathryn Mayorga wata yar kasar Amurka a shekara ta 2009.


Yan Sandan Las Vegas sun bukaci wannan dan wasa da ya bayar da hadin kai domin a gudanar da bincike daga kwayoyin halitar jikin dan Adam da aka sani da AND na sa, da za danganta da wanda ke saman rigar wannan mata a lokacin da suke tare a cewar masu bincike.

Dan wasan Cristiano Ronaldo ya musanta wannan zargi tareda bayyana cewa ,ya na daga cikin masu adawa da irin wadanan miyagun dabi’u da suka hada da fyade, ya kuma bayyana cewa ana kokarin shafa masa kajin kaji ne.