rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Amurka Isra'ila ‘Yan gudun Hijira Poland

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta shirya taro da ya yi ban hannu da manufofin Iran

media
Mike Pompeo Sakatary harakokin wajen Amurka tareda Ministan harakokin wajen Poland Jacek Czaputowic a Warsaw Janek SKARZYNSKI / AFP

A dai dai lokacin da Amurka ta kira taro dangane da kasar Iran tareda hadin gwiwar wasu kasashe 60 a Warsaw na kasar Poland, Ministan harakokin wajen Iran Mohammad Jayad Zarif ya yi watsi da zaman taron da Amurka da Poland suka shirya ,Ministan ya bayyana cewa zaman ba shida da wani tasiri.


Ministan harakokin wajen Iran Javad Zarif ya caccaki Amurka game da taron inda ya ce an shirya taron ne don ci gaba da kawo cikas ga manufofin kasar ta Iran .

Ministan ya bukaci a samu jituwa maimakon haka ana ci gaba da fuskantar turjiya daga Amurka da wasu kasashe 60 da zasu halarci taron na yau.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nuna gamsuwar sa dangane da wannan taro da zai mayar da hankali zuwa ga kasar ta Iran, yayinda Uwargida Federica Mogherini mai magana da yahun kungiyar tarrayar Turai ta szanar da cewa ba za ta halarci zaman taron na Warsaw ba.