rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Saudiya ta yi watsi da binciken kasa da kasa kan kisan Kashoggi

media
Jamal Khashoggi dan jaridar Saudiya da ya bace bayan shiga ofishin kasar Saudiya a Turkiya REUTERS/Simon Dawson

Saudiya ta yi watsi da bukatar baiwa tawagar jamiā€™ai masu zaman kansu na kasa da kasa, damar gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yiwa dan jarida Jamal Kashoggi, dan asalin kasar, a ofishin jakadancinta da ke Turkiya a shekarar bara.


Bandar Al-Aiban, shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Saudiya, ya shaidawa zauren majalisar dinkin duniya cewa, suna daukar dukkan matakan da suka dace dangane da bincike kan kisan gillar da kuma zakulo wadanda suka aikata shi.

Jawabin na Aiban ya zo ne bayan da a makon da ya gabata, kasashe 36 suka bukaci Saudiya ta bada damar gudanar da sahihin bincike mai zaman kansa kan kisan gillar da aka yiwa Jamal Kashoggi a farkon watan Oktoban bara.