Isa ga babban shafi
Turai

An gudanar da jana’izar Musulmin Bosnia 86

Daruruwan mutane ne yau suka halarci jana’izar Musulmin Bosnia 86 da dakarun Sabiya suka yiwa kisan gilla shekaru 27 da suka gabata a Prijedor, abinda ya haifar da yakin Bosnia na shekarar 1990.

Jana’izar Musulmin Bosnia 86
Jana’izar Musulmin Bosnia 86 ©REUTERS/Dado Ruvic
Talla

An dai samu gawarwakin mutanen wadanda akasarin su maza ne da kuma yara kanana a wani katafaren kabari a shekarar 2017 a Koricanske Stijene dake tsaunukan Bosnia.

Mutanen na daga cikin fararen hula Bosniyawa Musulmi sama da 200 da aka yiwa kisan gilla a Yankin.

Wannan na daga cikin yakin kabilanci mafi muni da aka gani tsakanin shekarar 1992 zuwa 1995 da ya lakume rayuka sama da dubu 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.