rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shekaru 50 da harba tauraron dan Adam na Apollo 11

media
Dan Adam a duniyar wata Harrison H. SCHMITT / NASA / AFP

A kasar Amurka an gudanar da gagarumin biki domin tunawa da cika shekaru 50 da harba tauraron dan adam na Apollo 11 zuwa duniyar wata, karo na farko a cikin tarin dan adam.

An dai kashe makudan kudade da kuma share tsawon shekaru kafin harba wannan kumbo a ranar 20 ga watan Yulin shekarar 1969


Daya daga cikin manyan injiyoyi a hukumar Nasa, Tom Scott, ya bayyana cewa muhimmin abu ne da ake tunawa da shi a wannan wuri, domin rana ce da dan adam ya tashi daga doron kasa zuwa wata duniya ta daban, wannan rana ce da ya kamata Duniya baki daya ta yi murna dangane da zagayowarta, sannan kuma a jinjina wa wadanda suka yi wannan kokari.

Kusan mutane dubu 400 ne suka share tsawon shekaru suna wannan aiki, tun daga bincike, gwaje-gwaje, kerawa da kuma harba wannan tauraro zuwa sararin samaniya.

Wannan aiki ne da ya taimaka sosai wajen samar da sauyi da kuma habaka bincike a fagen kimiya, saboda haka akwai hujjojin da za a iya gabatarwa da ke bayyana dalilan kashe makudan kudade da kuma kokari domin samuwar wannan nasara.