rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

lafiyar jama'a, zancen da yan takarar Democrat suka mayar da hankali

media
Muhawarar yan takarar jam'iyyar Democrat, Bernie Sanders, Joe Biden da Elizabeth Warren a Amurka REUTERS/Mike Blake

Matanen dake neman ganin Jam’iyyar Democrat dake Amurka ta tsayar da su takarar zaben shugaban kasa domin fafatawa da shugaba Donald Trump a shekara mai zuwa, sun kara da junan su a mahawara ta 3, inda batun kula da lafiyar jama’a ya mamaye mahawarar.


Tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden ya gamu da suka sosai daga sauran yan takarar musamman Sanata Bernie Sanders da Elizabeth Warren wadanda suke bin sa a baya a kuri’ar jin ra’ayin jama’a, a mahawarar da aka tafka a Houston dake Jihar Texas.

Bernie Sanders ya bayyana muhimmancin ganin Jam’iyyar Democrat ta kada shugaba Trump a zabe mai zuwa, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba kasa mafi hadari a tarihin Amurka.