rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ma’aikatan jirgin kasa sun tsunduma cikin yajin aiki a Faransa

media
Birnin Paris na kasar Faransa GERARD JULIEN / AFP

Mazauna birnin Paris dake Faransa yau sun fada cikin halin kakanikayi,sakamakon yajin aikin da ma’aikatan sufurin jiragen kasa suka tsunduma domin nuna rashin amincewar su da yunkurin yiwa dokar fansho gyaranfuska.

Matakin da ya haifar da cinkoson ababan hawa da kuma tilastawa
wasu jama’a zama a gidajen su.


Rahotanni sun ce an rufe 10 daga cikin hanyoyin jiragen kasa 16 dake zirga zirga a birnin Paris, yayin da aka dakile ayyuka a sauran guda 6.

Daruruwan mutane sun yi dafifi a tashoshin dake aiki musamman lokacin da jama’a suka yi sammako zuwa wuraren ayyukan su.

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace wasu daga cikin jama’a sun koma amfani da kekunan hayar da ake amfani da su domin zuwa wurin aiki.

Yajin aikin shine karo mafi girma da ma’aikata keyi domin nuna adawa da shirin shugaba Emmanuel Macron na yiwa dokar fansho gyara domin kawar da kamfanonin dake yiwa kowacce kungiya aiki.