Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta karrama sojojin ta da suka mutu a Mali

A birnin Paris, yau litinin za a gudanar da addu’o’in karrama sojojin Faransa 13 da suka mutu a hatsarin jirgin sama cikin makon da ya gabata a arewacin kasar Mali.Ma’aikatar tsaron Faransa ta fitar da sanarwar da ke nisanta hadarin jiragen yakinta biyu a Mali da ya hallaka sojin kasar 13 da farmakin mayakan jihadi.

Wurin da za gudanar da addu'o'in sojan Faransa a Paris  da aka kashe a Mali
Wurin da za gudanar da addu'o'in sojan Faransa a Paris da aka kashe a Mali Rfi / Anne-Marie Bissada
Talla

Za a dai gudanar da addu’o’in ne karkashin jagorancin shugaba Emmanuel Macron da kuma takwaransa na Mali Ibrahim Boubacar Keita. To sai dai shugaban na Mali na shan kakkausar suka a cikin gida, lura da cewa a cikin makonnin biyu da suka gabata an kashe sojojin kasar sama da 100 amma ba tare da an shirya masu wata jana’iza irin ta karramawa ba.

Fadar Shugaban kasar Mali na kokarin kare manufofin gwamnatin kasar duk da suka da take sha daga kungiyoyi da yan siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.