Isa ga babban shafi
Pakistan

Mutane 20 sun mutu a wurin ibadar Sufaye

An kama wani babban limamin wurin ibadar Sufaye da wasu mataimakansa biyu bisa laifin hannu a kisan mabiyansa ashirin da suka je ibada a safiyar yau lahadi.

Mutane akalla ashirin ne suka mutu yau a wurin ibadar Sufaye dake jahar Punjab a Pakistan
Mutane akalla ashirin ne suka mutu yau a wurin ibadar Sufaye dake jahar Punjab a Pakistan REUTERS/Akhtar Soomro
Talla

Mutumin mai suna Abdul Waheed mai shekaru hamsin ya aikata kisan ne ta hanyar sassara mutanen da adda.

Mazauna jahar Punjab yankin da al’amarin ya auku sun matukar nuna kaduwarsu kan aukuwar wannan kisa na ba gaira ba dalili.
Mata hudu na daga cikin wadanda limamin ya hallaka daya bayan daya inji masu bincike.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.