Isa ga babban shafi
Pakistan

An kashe mutane a masallacin jumma'a na Pakistan

Wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 23 tare da jikkata fiye da 30 a harin da ya kaddamar kan musulmi da ke sallar jumma’a a arewa maso yammacin Pakistan.

Mutane 23 sun mutu sakamakon harin kunar bakin wake a wani masallacin jumma'a da ke Pakistan
Mutane 23 sun mutu sakamakon harin kunar bakin wake a wani masallacin jumma'a da ke Pakistan Catherine MARCIANO / AFP
Talla

Lamarin ya faru ne a kauyen Butmaina da ke yankin kabilar Mohmand, kuma a kusa da kan iyakar Afghanistan, in da sojoji ke fafatawa da mayakan Taliban.

Mataimakin shugaban ‘yan sandan yankin, Naveed Akbar, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP da harin, in da ya kara da cewa, maharin ya shigo masallacin ne a dai-dai lokacin da aka tayar da salla.

Tuni dai aka kafa dokar hana zirga-zirga a yankin, bayan Firaministan kasar, Nawaz Sharif ya yi Alla-wadai da farmakin, kuma ya jaddada matsayin gwamnati na ci gaba da yakar ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.