Isa ga babban shafi
Pakistan

An kai harin kunar bakin wake a kotun Pakistan

‘Yan Sanda a kasar Pakistan sun ce mutane 11 suka mutu wasu 40 suka jikkata lokacin da wani dan kunar bakin wake ya jefa gurneti ya kuma tada bam a wata kotu da ke garin Mardan a yau Juma’a.

Rundunar  Sojin kasar Pakistan ta kashe wasu ‘yan kunar bakin wake 4 da ke kokarin kai hari kan wata unguwa ta kiristoci a wajen birnin Peshawar
Rundunar Sojin kasar Pakistan ta kashe wasu ‘yan kunar bakin wake 4 da ke kokarin kai hari kan wata unguwa ta kiristoci a wajen birnin Peshawar REUTERS/Fayaz Aziz
Talla

Faisal Shehzad, jami’in ‘Yan Sandan yankin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar an kai harin ne kan lauyoyi da ke kotun.

Akwai ‘Yan sanda biyu da lauyoyi cikin wadanda suka mutu a harin.

Zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin. Wannan kuma na zuwa ne bayan harin da aka kai a Quetta inda aka kashe lauyoyi da dama.

Kasar Paksitan dai na fama da hare haren kungiyar Taliban.

Kuma harin na ranar Juma’a na zuwa ne bayan rundunar Sojin kasar Pakistan ta kashe wasu ‘yan kunar bakin wake 4 da ke kokarin kai hari kan wata unguwa ta kiristoci a wajen birnin Peshawar a yau Juma’a.

Rundunar sojin kasar ta ce jami’anta da taimakon jiragen sama sun yi musayar wuta da maharan kafin hallaka su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.