Isa ga babban shafi
Saudiya

An fara Shari'a kan kamfanin Binladen sakamakon mutuwar Mahajjata

A kasar Saudiyya an fara shari'ar  Kamfanin daya mallaki kugiya ta gine-gine da ta haifar da hatsari da kashe mutane sama da 100 yayin aikin hajji na bara. 

Kayan aikin gini da ya fadawa Alhazai a Masallacin Makka.
Kayan aikin gini da ya fadawa Alhazai a Masallacin Makka. rfi
Talla

Ana zargin kamfanin daya mallaki kayan aikin ginin da sakaci da ya kaiga rasa rayukan jama’a, da kuma lalata kayayyaki a lokacin da kungiyar ta fado kan masu aikin ibada.

Wadan da ake zargi sun hada da wani attajiri na kasar Saudiyya, tare da wasu ‘yan kasashen Pakistan, Philippines, Canada da wasu da yawa daga kasashen Larabawa.

Hatsarin da ya auku a Babban Masallacin Makka yayi sanadiyyar mutuwar mutane 108, da jikkata wasu 400 da suka hada da yawanci Alhazai daga kasashen duniya.

Bayan aukuwan hatsarin Sarki Salman ya dakatar da kamfanin dake aikin – Saudi Binladen Group, saboda zargin akwai sakaci daga kamfanin.

Baya ga wannan hatsari a lokacin aikin hajjin na bara an sami turereniya wajen jifan Shaidan inda mutane samada 2,300 suka mutu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.