Isa ga babban shafi

Amurka ta kwashe likitocin kasarta 17 da ke makale a yankin Gaza

Amurka ta kwashe likitocin 17 ‘yan kasarta daga Gaza, bayan da  suka makale tun lokacin da Isra'ila ta mamaye mashigar Rafah.

Amurka ta kwashe likitocin 17 ‘yan kasarta daga Gaza, bayan da  suka makale  yankin.
Amurka ta kwashe likitocin 17 ‘yan kasarta daga Gaza, bayan da suka makale yankin. © AF
Talla

Jami'an diflomasiyyar Amurka ne suka  tsara yadda likitocin 17 za su fice daga yankin ta hanyar Karem Abu Salem da ta tsallaka cikin Isra'ila.

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin, ta shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, wasu likitocin Amurka uku da ke aikin sakai na kula da marasa lafiya sun ki ficewa daga yankin, duk kuwa da cewa babu tabbas na sake samun wata kafar da za su iya bi don fita daga yankin.

Mashigar Rafah da ta kasance daya tilo da ake amfani da ita wajen shigar da kayayyaki da mutane daga Gaza zuwa Masar, sai dai tun bayan sanarwar kwace ta daga hannun Hamas da Isra’ila ta yi a ranar 7 ga wannan watan da muke ciki, mashigar ta kasance a rufe.

Ma'aikatar kula da kiwon lafiya Gaza ta ce kawo yanzu mutane dubu 35,386 ne suka rasa rayukansu, tun bayan faro rikicin tsakanin Hamas da Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.