Isa ga babban shafi

Amurka ta hau kujerar naƙi game da bukatar samar da 'yantacciyar kasar Falasɗinu

Amurka ta sake hawa kujerar naƙi game da buƙatar bai wa yankin Falasɗinu damar zama kasa mai cikakken ƴanci da kuma kujerar dindindin a zauren Majalisar.

Zaman kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya gudana a birnin New York.
Zaman kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya gudana a birnin New York. © Yuki Iwamura / AP
Talla

Yayin zaman kaɗa ƙuri’ar da ya gudana a jiya Alhamis a birnin New York wanda kasashen Birtaniya da Switzerland suka kauracewa, kasashe 12 ne suka goyi bayan ƙudirin yayinda Amurkan ta sake jan tunga game da batun.

Bayan da ta yi watsi da ƙuri’un da takwarorinta suka kaɗa, Amurkan ta bakin mataimakin jakadanta a zauren Robert Wood ya ce yankin na Falasɗinu ba shi da zaɓin da wuce sulhuntawa da Isra’ila game da bukatar ta samun ƴanci ko kuma zama ƙasa mai cin gashin kanta.

A cewar Wood dukkanin yunƙurin da kasashe ke fafutukar yi ba zai haifarwa Falasɗinu ɗa mai ido ba, domin kuwa wannan yunƙuri ba shi ne zai kai yankin ga zamowa ƙasa mai cikakken iko ba.

Zaman kaɗa ƙuri’ar na zuwa ne bayan Isra’ila ta shafe fiye da watanni 6 ta na luguden wuta a zirin Gaza wanda ya kashe Falasɗinawa fiye da dubu 33 tare da tagayyara al’ummar yankin baya ge jefasu a matsanancin halin bukatar agaji.

Akalla kashi 2 bisa 3 na mambobin kwamitin tsaro na Majalisar ko kuma kasashe 9 cikin 15 na zauren ake bukata su kada ƙuri’ar amincewa ƙudiri gabanin kasancewarsa doka, sai dai a wannan karon lamarin ya sha bamban.

Duk da yadda kasashe 12 suka kaɗa ƙuri’ar amincewa da ƙudirin, hawa kujerar naƙin da Amurka ta yi ya kashe fatan da ake da shi na kawo karshen rikicin Isra’ila da Falasɗinu, batun da mai sharhi kan siyasar duniya na Aljazeera Marwan Bishawa ke cewa Amurka za ta sahale kasancewar Falasɗinu kasa mai cin gashin kanta ne kaɗai a lokacin da ta yi niyya.

Kafin wannan zaman kaɗa ƙuri'a dai shugaba Joe Biden na Amurka da kansa ya bayyana cewa samar da ƙasar Falasɗinu shi ne hanya ɗaya tilo na warware rikicin yankin da Isra'ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.