Isa ga babban shafi

Mutane kusan miliyan 300 suka fuskanci bala'in yunwa a 2023 - MDD

Wani rahoton kwararru da aka tattara a karkashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda kuma aka wallafa shi a ranar Laraba, ya ce yawan waɗanda suka faɗa ƙangin yunwa ya karu zuwa kusan mutane, miliyan 300 a cikin shekarar 2023.

Buhunan abinci na Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya
Buhunan abinci na Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya AFP Photos/Sia Kambou
Talla

Rahoton wanda ya ce karo na biyar kenan da ake fuskantar karuwar yawan mutanen da ke fuskantar yunwa a duk shekara tun daga 2019 kenan, ya dora alhakin karuwar matsalar da ta shafi sassan duniya akan tashe-tashen hankula, da bala’o’in ambaliyar ruwa, da fari sakamakon tasirin Sauyin Yanayi, sai kuma durkushewar tattalin arzikin kasashe da dama.

Ya zuwa yanzu mutane kusan miliyan 282 rahoton kwararrun ya ce sun yi fama da yunwa a shekarar 2023, bayan samun karin mutane miliyan 24 da suka faɗa cikin ƙangin, idan aka kwatanta da adadin da aka samu a shekarar 2022.

Masanan da suka wakilci hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya, da Ƙungiyar Tarayyar Turai, da kasashe, da kuma kungiyoyin kasa da kasa, sun ce kasashen da al’umominsu suka fi fuskantar yunwar sun haɗa da Afghnaistan, da Jamhuriyar Dimokadiyyar Congo, da Habasha, da Najeriya da Syria da kuma Yemen.

Rahoton ya kuma bayyana Zirin Gaza da Sudan da Haiti, da Zimbabwe da kuma Malawi cikin waɗanda ke buƙatar agajin gaggawar karshen kuncin na karancin abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.