Isa ga babban shafi

An kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Haiti

An rantsar da majalisar da ke da alhakin zabar sabon firaminista da majalisar ministocin kasar Haiti mai fama da rikici a ranar Alhamis.

Michel Patrick Boisvert kenan daga tsakiya.
Michel Patrick Boisvert kenan daga tsakiya. AP - Ramon Espinosa
Talla

Sai dai rahotanni sun ce, ba a gudanar da bikin rantsar da majalisar rikon kwarya ba a fadar gwamnatin da ke babban birnin kasar saboda fargabar hare-haren 'yan daba.

Ministan tattalin arzikin kasar, Michel Patrick Boisvert, shine aka nada a matsayin firaministan rikon kwarya a halin yanzu.

A kwanakin baya, motoci masu sulke sun yi ta shawagi a harabar ginin gwamnatin.

A kowace rana, ana jiyo amon Harbin bindiga da kuma wucewar harsasai a babban birnin kasar, abin da ya jefa al’umma ccikin fargaba ainun.

Caseus, wani mazaunin yankin, ya shaidawa Reuters cewa bai taba ganin Haiti cikin irin wannan matsala ta rashin tsaro ba.

Tun daga shekarar 1986 kasar fuskantar matsalolin tsaro, musamman ‘yan dabar da ke dauke da makamai.

A ranar Alhamis din ne, tsohon firaminista Ariel Henry ya mika takardar murabus din gwamnatinsa a hukumance daga Los Angeles na kasar Amurka, inda yake gudun tsira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.