Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da suka wuce shekaru 100 a Faransa ya zarce dubu 31

FARANSA – An samu karuwar yawan mutanen dake zarce shekaru 100 a raye a kasar Faransa kamar yadda rahotan binciken hukumar dake kula yawan jama'a ya nuna.

Shugaban Faransa Emamnuel Macron
Shugaban Faransa Emamnuel Macron © Christophe Petit Tesson/AFP
Talla

Rahotan yace binciken da aka gudanar ya nuna an samu karuwar mutanen da aka yiwa suna 'supercentenarians' ko kuma wadanda suka zarce shekaru 100 a duniya, yayin da wasu daga cikin su suka kai shekaru 110.

Rahotan yace a shekarar 1900 akwai akalla dattawa 100 da shekarun su ya zarce 100 a duniya, wadanda daga bisani suka ribanya zuwa 200 shekarar 1950.

Binciken yace a shekarar 1970 an samu mutanen da suka zarce shekaru 100 a Faransa da yawan su ya kai sama da dubu guda, yayin da a shekara ta 2000 adadin ya zarce dubu 8.

Rahotan yace a wannan shekara alkaluma sun nuna cewar akwai tsoffin da suka zarce shekaru 100 a duniya da yawan su ya wuce dubu 31, abinda ya nuna cewar alkaluman ya ribanya abinda aka saba gani a shekara ta 2000 har sau 4.

Bincike yace idan aka ci gaba da ganin haka, nan da shekara ta 2070, adadin mutanen da zasu wuce shekaru 100 a duniya a kasar Faransa zai zarce dubu 200.

Daya daga cikin mutanen da suka gudanar da binciken, Laurent Toussant ya bayyana halayyar irin wadannan mutane da suka hada da masu motsa jiki da masu cin abinci na musamman.

Masu binciken sun ce sun gano wasu daga cikin irin wadannan mutane a tsibirin Guadeloupe da Martinique dake karkashin ikon Faransa.

Yanzu haka gwamnatin Faransa na shirin bikin ranar haihuwar matar da ta fi kowa yawan shekaru a kasar da ake kira Marie-Rose Tessier, wadda zata cika shekaru 114 a ranar 21 ga watan Mayu mai zuwa.

Alkaluma sun bayyana cewar wata 'yar kasar Spain da ake kira Maria Branyas Morera ce tafi kowa tsufa a duniya da shekaru 117 yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.