Isa ga babban shafi

Martanin kasashe kan wa'adin da Isra'ila ta bai wa Faladinawa na ficewa a Gaza

Kasashen duniya da mayan kungiyoyi sun yi Allah wadai game da wa'adin sa’o’i 24 da Isra'ila ta ba wa mazauna Gaza kimanin miliyan daya da ta ba su fice daga birinin zuwa kudancin yankin gabar tekun, akokarin kaddamar da mamaya.

Sojojin Isra'ila dake shirin yi wa Gaza kawanya.
Sojojin Isra'ila dake shirin yi wa Gaza kawanya. REUTERS - RONEN ZVULUN
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an sanar da ita wannan batu tun tsakar dare, amma sojojin Isra’ila sun tabbatar da jinkirta farmakin yayin da mazauna Gaza suka shiga wani yanayi na firgici, inda dubban mutane ke tururuwa ta hanyar tattaki ko ababen hawa domin ficewa kafin cikar wa’adin.

Ga martanin wasu kasashen:

Amurka

Fadar gwamnatin Amurka ta White House wadda babbar kawa ce ga kasar ta Yahudawa ta ce matakin na Isra’ila rashin hankali ne.

Kakakin Kwamitin Tsaron Amurka John Kirby ya shaida wa CNN cewa, ba’a bukatar wannan umurni a hakin da yankin ke ciki.

Sojojin Isra'ila kan hanyar zuwa Gaza.11/10/23
Sojojin Isra'ila kan hanyar zuwa Gaza.11/10/23 AP - Ohad Zwigenberg

Wani jami’in Amurka ya ce, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken na aiki tare da Isra'ila domin ganin an samar da tudun mun tsiri ga fararen hula ta yadda farmakin Isra’ila bazai shafe sub a.

Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana bukatar fitar da mutane cikin kankanin lokaci da cewa ba abin lamunta ba ne, inda ta bukaci Isra'ila da ta yi watsi da Shirin.

Ta na mai cewa zata mayar da hukumarta na 'yan gudun hijirar Falasdinu da ma'aikatan kasashen waje zuwa kudancin Gaza.

Kungiyar Red Cross

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce mazauna Gaza ba su da wani wuri dake da tsaro, kuma basu da tabbas kan ko inda aka tura su yanzu bazai fuskanci hari ba.

Wata 'yar falasdin da harin Isra'ila ya rutsa da ita a Gaza
Wata 'yar falasdin da harin Isra'ila ya rutsa da ita a Gaza REUTERS - IBRAHEEM ABU MUSTAFA

 Kasar Turkiyya 

Turkiyya ta ce bukatar Isra’ila na kwashe mutanen ba abin lamunta ba ne.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce, "Tilastawa mazauna Gaza miliyan 2.5, wadanda suke fama da munanan hare-haren  har tsawon kwanaki da kuma hana musu wutar lantarki, ruwan sha da abinci, tilasta musu yin hijira zuwa a wannan yanayi, wani lamari ne da ya saba wa dokokin kasa da kasa, kuma cin zarafin bil'adama ne.

Hukumar Lafiya ta Duniya

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, jami'an Falasdinawa sun shaida mata cewar daukar marasa lafiya da gajiyayyu zuwa kudancin zirin Gaza abu ne mai mutukar wuya.

 

Wasu Falasdiwa da harin Isra'ila ya yi ajalinsu
Wasu Falasdiwa da harin Isra'ila ya yi ajalinsu AP - Fatima Shbair

Kakakin WHO Tarik Jasarevic ya bayyana cewar asibitoci a kudancin Gaza sun riga sun cika makil yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare da sama, fararen hula ba su da wani wurin mai tsaro da ya rage da za su je.

Hukumar Falasdinawa

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya yi gargadin cewa matakin wani shiri na maimata "Nakba na biyu" wato korar Falasdinawa kusan 760,000 daga gidajensu A 1948, lokacin da aka samar da Isra'ila.

Abbas ya ce ya yi watsi da wannan batu fitar da mutane daga zirin Gaza, domin hakan zai zama tamkar Nakba na biyu a cewarsa

Kungiyar Larabawa 

Kungiyar hadin kan Larabawa mai hedkwata a birnin Alkahira ta yi Allah wadai da matakin wanda ta ce aikata babban laifi.

Ahmed Abul Gheit yayin taron kungiyar kasashen larabawa
Ahmed Abul Gheit yayin taron kungiyar kasashen larabawa AFP

Jagoran kungiyar Ahmed Abul Gheit ya zargi Isra'ila da azabtar da fararen hula marasa galihu a Gaza da sunan ramuwa, maimakon tsara ko nazari kan hanyoyin yakar mayakan Hamas saboda munanan hare-haren da suke kai wa kasar Isra'ila.

Kasar Masar 

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya bukaci al'ummar Gaza da su dage wajen tsayawa a kasarsu, a daidai lokacin da ake kira ga Alkahira da ta ba wa fararen hula damar ficewa zuwa tudun mun tsiri daga Gaza.

Shugaban kasar Masar Abdel Fatah Al Sisi
Shugaban kasar Masar Abdel Fatah Al Sisi © Mandel Ngan / AP

Jami'an Amurka sun ce suna tattaunawa da Masar domin bude mashigar Rafah ga 'yan kasashen waje da ke son ficewa.

Kasar Jamus

A wani taron manema labarai yayin wata ziyara da ta kai birnin Kudus, ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta yi Allah wadai ga kungiyar Hamas da ta ce ta yi garkuwa da daukacin al'ummar Gaza.

Kasar Rasha

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kwatanta kawanyar da Isra'ila ta yi wa Gaza da 'yan Nazi da suka yi wa birnin Leningrad a yakin duniya na biyu.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin AP - Mikhail Metzel

Ya ce ya fahinci take-taken Isra’ila kan Gaza, kuma ba abin amincewa ba ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.