Isa ga babban shafi

Falasɗinawa na tunawa da 'Nakba' yayin da dubbai ke tserewa daga Rafah

Dubun dubatan fararen hula ne suka tsere daga birnin Rafah na kudancin Gaza gabanin barazanar kutsawa cikin birnin ta ƙasa da dakarun Isra’ila suka yi, a yayin da a wannan Laraba Falasɗinawa ke bikin ‘Nakba’, don tunawa da bala’in da ya same su a shekarar 1948.

Falasɗinawa a yayin tunawa da ranar 'Nakba'.
Falasɗinawa a yayin tunawa da ranar 'Nakba'. REUTERS - MAJA SMIEJKOWSKA
Talla

A yayin yaƙin da ya samar da ƙasar Isra’ila, kimanin Falasɗinawa dubu dari 7 da 60 ne aka kora daga gidajensu, kana da dama suka nemi mafaka a inda yanzu ya kasance Zirin Gaza da yankin Yamma da Kogin Jordan.

Bikin tunawa da ranar ‘Nakba’ na zuwa ne a yayin da faɗan da ake gwabzawa ta fuskoki dabam-dabam a tsakanin dakarun Isra’ila da mayaƙan Hamas a fadin Zirin Gaza, ya tilasta wa Falaɗinawa da dama barin muhallansu.

Tun daga ranar 6 ga watan Mayu, kusan Falaɗinawa dubu ɗaeri 4 da 60 ne aka ɗaiɗaita daga Rafah, da kuma kimamin dubu 100 daga arewacin Gaza, kamar yadda majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.

Hakan na nufin cewa kimanin rabin-rabin al’ummar Gaza da adadin su ya kai miliyan 2 da dubu ɗari 4 ne aka ɗaiɗaita a cikin mako guda.

Ƙawanyar da aka wa wannan yankin sakamakon yaƙin ta haddasa matsalar jinƙai, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ke nanata kashedin cewa aana daf da shiga matsanacin ƙarancin abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.