Isa ga babban shafi

Magatardan MDD ya nemi Isra'ila ta daina zubar da jinin Falasɗinawa

Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga Isra’ila da ta gaggauta buɗe dukkanin iyakokin shiga Zirin Gaza da ta garƙame, ta kuma dakatar da hare-haren da ke ci gaba da laƙume rayukan Falasɗinawa.

Antonio Guterres,, maga takardan Majalisar Ɗinkin Duniya.
Antonio Guterres,, maga takardan Majalisar Ɗinkin Duniya. © Brendan McDermid / Reuters
Talla

Guteress yayi kiran ne jim kaɗan bayan da tankokin yaƙin Isra’ila suka kutsa cikin Rafah, garin da ya kunshi Falasɗinawa ‘yan gudun hijira fiye da miliyan 1 da dubu 200.

Wannan mataki na Isra’ila na zuwa ne bayan da a jiya ta tilasta wa Falasdinawa akalla ko kuma sama da dubu 100 barin gabashin yankin wannan birni na Rafah, wanda a yanzu kuma ta ke iko da iyakarsa, matakin da shi Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ke kokawa akai, duba da yadda ya daƙile duk wani kokari na shigar da kayayyakin agaji zuwa cikin birnin mai ɗauke dubun dubatar Falasdinawa ‘yan gudun hijira.

A halin da ake ciki tsaye iyakar Rafaha ko mashiga kamar yadda ake kira ta koma ƙarƙashin ikon Isra’ila, abinda ke nufin babu wanda ya isa ya ketara cikin kasar Masar daga Gaza ko kuma daga cikin Masar zuwa Gaza ba tare da amincewar dakarunta ba.

Wannan iyaka ta Rafah da ta raba Gaza da Masar, ita ce ragowar iyakar kan tudu guda ɗaya da ta rage, wadda ƙungiyoyin agaji ke amfani da ita wajen shigar da tallafi zuwa Falasdinawa a Zirin Gaza.

Baya ga kaɗuwa, koke da kuma kira da Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya yayi, kungiyar EU ma gargaɗi ta yi kan girman tashin hankalin da ke tafe, la’akari da yiwuwar salwantar rayukan wasu ƙarin dubban Falasdinawa da za a samu.

 Babban jami’in kula da harkokin ƙasashen wajen kungiyar kasashen Turan, Josep Borell ya yi gargaɗin cewa a halin yanzu fa, Falaɗinawa ba su da wurin gudu don tsira, zalika yanzu haka ƙananan yara dubu 600 ne ke birnin na Rafah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.