Isa ga babban shafi

Sama da mutane dubu 250 sun arce daga Gaza a yayin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta

Isra’ila ta ci gaba da yin luguden wuta a kan yankin Zirin Gaza a kwana ta 5 a jere, inda a wannan Laraba, dukkannin gundumomin yankin suka kasance tamkar kufai, a yayin da adadin wadanda suka mutu ke karuwa.

Hayaki da ya turnike sararin samaniya kenan a yankin Zirin Gaza bayan hare-haren Isra'ila a Larabar nan.
Hayaki da ya turnike sararin samaniya kenan a yankin Zirin Gaza bayan hare-haren Isra'ila a Larabar nan. AFP - MOHAMMED ABED
Talla

Rundunar sojin Isra’ila ta ce an gano gawarwaki dubu 1 da dari 2, wadanda akasarinsu fararen hula ne, a yayin da mahukuntan Gaza suka sanar da cewa sun rasa mutane dari 9 a wannan ya ke da ya barke biyo bayan harin da kungiyar HAMAS ta  kai cikin Isra’ila.

Isra’ila ta jibge dakaru da tankunan yaki da sauran motocin yaki da manyan makamai a kewayen Gaza, a kokarin da ta ke na abin da fira minista Benyamin Netanyahu ya kira ‘ramuwar  gayya a kan hari mafi girma da aka kai wa Yahudawa tun bayan kisan kare dangi da aka musu shekaru da dama da suka wuce’.

Shugaban Amurka Joe Biden, wanda ya caccaki wannan hari da aka kai wa Isra’ila, ya sha alwashin taimaka mata da Karin kayayyakin yaki.

Hankula na ci gaba da tashi duba da yadda matsalar jinkai ke rincabewa a yankin Zirin Gaza da yaki ya daidaita, ganin yadda Isra’ila ta ruguza gidaje sama da dubu 1, bayan yi masa kawanya, tare da yanke wutar lantarki da ruwa da abinci ga  mutane miliyan 2 sa dubu dari 3 da ke yankin.

Sama da mutane dubu dari 2 da 60 ne suka arce daga gidajensu sakamakon hare-haren na Isra’ila, a cewar Majalisar Dinkin Duniya, a yayin da Tarayyar Turai ke kira da a samar da wata  kafa da za ta bai wa fafaren hular da ke tserewa damar yin haka a yaki na 5 cikin shekaru 15.

Yanzu alamu na nuni da cewa Isra’ila na shirin mamayar yankin Zirin Gaza  ta kasa, sai dai tana fuskantar  barazanar hare-hare daga kusurwowi da dama, bayan da ita ma kungiyoyi masu dauke da makamai suka kai mata hare-haren rokoki daga Lebanon da Syria a wannan Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.