Isa ga babban shafi

Isra'ila ta kai harin bama-bamai a Lebanon da zirin Gaza

Sojojin Isra'ila sun kai hari kudancin Lebanon da zirin Gaza a daidai lokacin da Firaministan Isra'ila ke cewa abokan gabarsu za su dandana kudarsu bayan da ya zargi mayakan Hamas da kai hare-haren rokoki kan Isra'ila.

Wasu gine-gine dake ci da wuta a yankin Gaza bayan harin Isra'ila
Wasu gine-gine dake ci da wuta a yankin Gaza bayan harin Isra'ila AFP - MOHAMMED ABED
Talla

Dakarun sojin Isra'ila sun kai harin ne  wasu wurare a Lebanon da Gaza da sanyin safiyar Juma'a, a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren rokoki da suka dora alhakinsa kan kungiyar Hamas, daidai lokacin da ake ta kai ruwa rana kan farmakin da 'yan sandan Isra’ila suka kai cikin masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus a makon nan.

Fashe-fashe masu karfi sun girgiza yankuna daban-daban na Gaza, a daidai lokacin da Isra'ila ta ce jiragenta sun kai farmaki kan wasu wurare da suka hada da na kera makamai na Hamas da kuma wasu hanyoyin da aka haka a karkashin kasa.

Rundunar sojin kasar ta ce ta kuma kai hari kan mayakan Hamas da ke kudancin kasar Lebanon, inda mazauna yankin da ke kusa da sansanin 'yan gudun hijira na Rashidiyeh suka sanar da tashin bama-bamai uku.

Harin rokoki zuwa Isra'ila

Harin dai ya zo ne a matsayin martani kan hare-haren rokoki da aka harba daga Lebanon zuwa yankunan arewacin Isra'ila, wanda jami'an Isra'ila suka dora alhakinsa kan Hamas. Rundunar sojin ta ce an harba rokoki 34 daga kasar Labanon, inda sukayi nasarar tare 25 daga cikinsu.

Wannan dai shi ne hari mafi girma da aka kai tun daga shekarar 2006, lokacin da Isra'ila ta gwabza yaki da kungiyar Hizbullah da ke dauke da muggan makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.