Isa ga babban shafi

Harin da Isra'ila ta kai Jabaliya ya hallaka kusan mutane 200 da jikkata 777

Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare-hare da Isra’ila ta kai sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya a yankin zirin Gaza wanda ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane 200 tare da bacewar sama da 100 na iya zama laifukan yaki.

Masu aikin ceto ke kokarin fitar da wata yarinya karkashin baraguzan gina da Isra'ila da kai wa hari a sansanin gudun hijara na Jabaliya dake Gaza, 01/11/23.
Masu aikin ceto ke kokarin fitar da wata yarinya karkashin baraguzan gina da Isra'ila da kai wa hari a sansanin gudun hijara na Jabaliya dake Gaza, 01/11/23. AP - Abed Khaled
Talla

A cikin kasa da sa'o'i 24, adadin wadanda harin bam na farko da na biyu na Isra'ila ya shafa a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia ya zarce 1,000 a cewar sabon rahoton da ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya wallafa.

Adadin ya hada da mutane 195 da aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da 777 suka jikkata, sannan har yanzu ana neman karin mutum 120 da suka bace.

Laifukan yaki

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana hare-haren da Isra’ila ta kai a ranakun Talata da Laraba a Jabalia a matsayin “mai ban tsoro”, yayin da hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar ta ce hare-haren na iya zama “laifun yaki”.

Anguwar Jabaliya Isra'ila ta kaiwa hari a zirin Gaza, 01/11/23.
Anguwar Jabaliya Isra'ila ta kaiwa hari a zirin Gaza, 01/11/23. © STRINGER / Reuters

Shugaban Amurka Joe Biden dake shan suka daga ciki da wajen kasar kan cin zali da kasar Yuhudun Isra’ila ke yi, wanda masu zanga-zanga suka yi ta katse masa jawabi yayin yakin neman zabe da yammacin Laraba, ya ce akwai bukatar dakatar da fadan na wani lokaci, domin kai kayan agaji, yaki fitowa ya ambaci tsagaita wuta.

Yayin da Faransa ta ce ta damu matuka game da hare-haren da Isra'ila ta kai a sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya a Gaza.

Fitar da baki da majinyata daga Gaza

Tuni 'yan kasashen waje na farko da kuma wasu Falasdinawa da dama da suka jikkata suka samu damar barin Gaza ta mashigar kan iyakar Rafah, yayin da aka  sanar da sunayen daruruwan mutanen da za su fita ta hanyar Rafah a zango na biyu.

Hukumar kula da kan iyakokin Gaza ta fitar da jerin sunayen 'yan kasashen waje 596 da na kasashen biyu daga kasashe 15 wadanda za a ba su izinin barin Gaza a wannan Alhamis.

Motocin daukar marasa lafiya na yankin Gaza a lokacin da suke ketawa zuwa Masar ta iyakar Rafah, 1 Nuwamba 2023.
Motocin daukar marasa lafiya na yankin Gaza a lokacin da suke ketawa zuwa Masar ta iyakar Rafah, 1 Nuwamba 2023. © AFP - MOHAMMED ABED

A halin da ake ciki kasar Masar ta ce za ta taimaka wajen kwashe 'yan kasashen waje 'kusan 7,000 da ke da fasfo daga Gaza.

Sama da mutum dubu 20 sun jikkata

Kungiyar Likitoci ta Duniya MSF ta ce, fiye da mutane 20,000 da suka samu raunuka har yanzu suna makale a zirin Gaza, duk da fara kwashe masu fasfo na kasashen waje da Falasdinawa da suka samu munanan raunuka ta kan iyakar kasar da Masar.

Alkaluman ma’aikatar lafiyar Gaza sun nuna cewa, aƙalla Falasɗinawa 8,796, ciki har da yara 3,648, farmakin sojan Isra'ila ya kashe a Zirin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba, a cewar sabon alkalumman ma'aikatar lafiya ta Gaza.

Katse alaka da Isra'ila

Wasu kasashe na yanke hulda da Isra'ila, domin nuna adawa da harin bama-bamai da kashe fararen hula a Gaza.

Kasa ta baya-bayan nan da Isra’ila itace Jordan, wanda ta kira jakadanta a Isra'ila ya koma gida, tare da korar na Isra’ila dake kasar, tana mai cewa za ta mayar da wakilinta ne kawai idan Isra'ila ta daina kashe fararen hula.

Sojojin Isra'ila dake kai farmaki yankin Gaza. 1/11/23
Sojojin Isra'ila dake kai farmaki yankin Gaza. 1/11/23 © JALAA MAREY / AFP

A daren Talata mataimakin ministan harkokin wajen Bolivia Freddy Mamani ya sanar da katse huldar diplomasiyya da kasar Isra'ila domin nuna kyama da kuma yin Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da Isra'ila ke kaiwa a zirin Gaza.

Makwabtanta Colombia da Chile suma sun kira jakadunsu tare da yin Allah wadai da mutuwar fararen hula a Gaza tare da yin kira da a tsagaita wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.