rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

India Amurka Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun India ta wanke mutum 35 da ake zargi da safarar makamai

media
Tun da farko a shekarar 2016 wata kotu ta yankewa mutanen hukuncin daurin shekaru biyar-biyar a gidan yari, sai hukuncin babbar kotun ya yi watsi da hukuncin na farko. CC/Wikimedia

Wata kotu a kasar India ta wanke wasu mutane 35 ciki harda ‘yan Britania da 'yan kasare Estonia da kuma Ukraine, wadanda ake zargin sun yi safarar tarin bindigogi zuwa kasar ta hanyar amfani da wani jirgin ruwan Amurka a shekarar 2013.


A shekarar 2016 ne wata kotun kasar ta daban ta yankewa mutanen su 35 hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari, sai dai kuma bayan daukaka kara kan hukunce yanzu haka Kotu ta wanke su.

Mutanen 35 da suka kunshi ‘yan kasar Britania 6 da ‘yan Ukraine 3 da kuma 'yan Estonia 14 tare da hadin gwiwar wasu Indiyawa 12, hukumomin kasar na zarginsu da safarar makamai a shekarar 2013 lamarin da ya sa aka gurfanar da su gaban kotu tare da yanke musu hukuncin daurin shekaru biya-biyar a gidan yari.

Tun da farko jami'an tsaron da ke gadin gabar tekun kasar ta India ne suka kama jirgin ruwan mallakin Amurka bayan da mutanen suka gaza bayyana nau'in kayakin da suka yi safara kuma su ke kokarin shigar da shi kasar.