rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Falasdinawa Isra'ila Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Fatah za ta yi zanga-zangar adawa da ziyarar Mike Pence Kudus

media
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas REUTERS/Eduardo Munoz

Kungiyar Fatah ta shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ta kira zanga-zanga a ziyarar da mataimakin shugaban kasar Amurka, Mike Pence ke shirin kai wa birnin Kudus a mako mai zuwa.


Kazalika Mahmoud Abbas ya sauke ganawarsa a mataimakin shugaban Amurkar, tare da gargadin cewar kasar ba ta da gurbi ko daman jagoranci tattaunawar sulhu tsakanin Falasdinu da Isra’ila.

A makon da ya gabata Shugaba Donald Trump na Amurka ya ayyana birnin na Kudus a matsayin baban birnin Isra’ila, batun da ya janyo suka daga kasashen duniya.