Isa ga babban shafi
Falesdinu

Falesdinu na ci gaba da samun goyan bayan kasashen musulmi

Shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniyeh ya kira kasashen musulmai na Duniya da su gudanar da zanga-zanga nuna goyan baya zuwa Falesdinawa dangane da matakin Shugaban Amurka na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin Isra’ila mako daya da ya gabata.

Taron kwamity tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York kan rikicin birnin Qudus
Taron kwamity tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York kan rikicin birnin Qudus REUTERS/Brendan McDermid
Talla

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana amincewarsa da matsayin Birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, a wani jawabi da ya sauya manufofin Amurka wanda yanzu haka ya haifar da tashin hankali a Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Trump ya ce Isra'ila kasa ce mai ‘yanci saboda haka tana iya sanya babban birnin ta inda ta ke so.

Trump ya ce matakin ba zai sauya matsayin Amurka na samun kasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasdinu ba idan sun amince a tsakanin su.

Tuni wannan batu na Mista Trump ya janyo suka daga shugabannin duniya daban-daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.