Isa ga babban shafi
Yemen-Saudiyya

Harin da Saudiyya ta kai a Yemen ya kashe mutane 14

Shaidun gani da ido sun ce harin da dakaru ƙarƙashin jagorancin Saudiyya suka kai a wata kasuwa da ke arewacin ƙasar Yemen ya kashe mutane 14.

Wani hari da aka kai a Yemen.
Wani hari da aka kai a Yemen. REUTERS/Naif Rahma TPX IMAGES OF THE DAY
Talla

A cewar kamfanin dillancin labaru da ke ƙarƙashin yan tawayen ƙasar, harin wanda aka kai ta sama a yammacin Laraba ya kashe mutane 12, yayin da aka kai hari na daban kan wani gida a yankin Baqim, wanda ya  kashe mutane 2.

Saudiyya na jagorantar dakarun ƙawance a Yemen tun cikin shekara ta 2015 a ƙokarin ta na dakatar da ƴan tawayen Huthi waɗanda suka ƙwace yankuna da dama a ƙasar.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane 9,000 ne suka mutu a ƙasar ta Yemen tun lokacin da dakarun suka ƙaddamar da yaƙi da ƴan tawayen na Huthi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.