Isa ga babban shafi

India na fuskantar bala'in karancin ruwa mafi muni a tarihinta

Hukumar rajin bunkasa ci gaban India NITI Aayog, ta ce a halin da ake ciki, kasar na fuskantar bala’in karancin ruwan sha mafi muni a tarihinta.

Wani rahoton masana ya ce akalla kashi 40% na al'ummar India za su fuskanci karancin ruwan sha mai tsafta nan da zuwa shekarar 2030.
Wani rahoton masana ya ce akalla kashi 40% na al'ummar India za su fuskanci karancin ruwan sha mai tsafta nan da zuwa shekarar 2030. Reuters/Amit Dave
Talla

Rahoton ya ce, bayanan da jami’ai suka tattaro a jihohi 24 daga cikin 29 da kasar, ya nuna cewa akalla ‘yan kasar ta India miliyan 600 ne suka fuskantar ba’la’in karancin ruwan, kuma babu alamun akwai sauki a nan kusa.

Hukumar ta Niti Aayog ta kuma yi gargadin nan da zuwa shekarar 2020, jihohi 21 daga cikin 29 na kasar ta India za su fuskanci kafewar ruwan da ke karkashin kasa.

Wannan bala’I dai kai tsaye zai shafi sha’anin noma a India, la’akari da cewa kusan kashi 80 na yawan ruwan tabkunan kasar ana amfani da shi ne wajen ayyukan gona.

A dukkanin lokutan tsananin zafi mafi akasarin al’ummar India na fuskantar karancin ruwa, sai dai wadanda ke zaune a karkara ne suka fi wahala.

Wani rahoto da hukumar bunksa kasar ta India ta Niti Aayog ta wallafa ya nuna cewa akalla ‘yan kasar 200,000 ke hallaka a duk shekara, sakamakon rashin ruwan sha mai tsafta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.