rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Japan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ruwan sama sun haddasa mutuwar mutane a Japan

media
Ruwan sama a kasar Japan rfi

Ruwan sama masu karfin gaske sun sauka a Japan inda suka haddasa cikas ga masu ayyukan ceto, Gwamnatin kasar ta bukaci jama'a yan kasar da su kauracewa gidajen su.


Ruwan sama mai karfin gaske ne ya sauka a Japan wanda hakan ya haifar da ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar.

A wannan karon ruwan na tafe ne da guguwa mai karfin gaske, kuma ta fi shafar gagaruwan Hiroshima,Kyoto, Okayama wadanda ambaliyar ta fi yin mumunan ta’adi.

Kawo yanzu alkaluma na bayyana cewa mutane 20 suka rasa rayukansu sakamakon wannan lamari.

Akwai mutane kusan milyan daya da suka kauracewa gidajensu, yayin da wasu da dama suka makale a wasu yankuna sakamakon yadda ruwa suka  yanke hanyoyin mota, turakun wutar lantarki da na wayar talho.