Isa ga babban shafi
Syria

Mutane na ci gaba da tserewa daga gabashin Syria

Sama da mutane dubu 11 ne suka baro gidajensu dake tingar karshe ta mayakan Kungiyar Isil a gabashin kasar Syria, mafi yawansu kuma iyalan mayakan jihadin ne, dake kokarin tserewa hare haren da hadakar dakarun larabawa da kurdawa .

Sansanin yan gudun hijira a kan iyka da Jordan
Sansanin yan gudun hijira a kan iyka da Jordan AP News
Talla

Rahoton na zuwa ne daga wata Kungiya mai zaman kanta dake zura ido a rikicin kasar ta Syria wacce ta sanar da haka a jiya alhamis.

A watan satumbar da ya gabata ne hadakar dakarun larabawa da kurdawa na Forces démocratiques syriennes (FDS) suka kaddamar da gagarumin hari kan mayakan jihadin kungiyar Isil a yankin Deir Ezzor, kusa da kan iyakar kasar Iraqi, tare da taimakon hadakar dakarun kasashen Duniya dake yakar duk wata kungiya dake ikararin jihadi a karkashin jagorancin kasar Amruka

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.