Isa ga babban shafi
Syria

Sojin Gwamnati sun kwace sansanin ‘yantawaye a Siriya

Sojin kasar Siriya sun yi nasarar kwace garin Yabrud da ke matsayin sansanin Yan Tawayen da ke neman kauda Gwamnatin shugaba Bashar al- Assad daga karagar mulki, yayin da rikicin kasar ya shiga shekara ta hudu ana gudanar da shi

Sojin kasar Siriya
Sojin kasar Siriya AFP PHOTO / Hannah McNeish
Talla

Wannan nasara da sojin Gwamnatin shugaba Bashar al Assad suka samu, ta zama wata gagarumar koma-baya ga ‘Yan tawayen kasar, wadanda ke ci gaba da rasa Yankunan da ke hannun su.

Wakilin kanfanin Dillancin labaran Faransa da ya shiga Garin, bayan Dakarun sun samu nasara, ya ga sojojin na shan iska, sakamakon galabar da suka samu.

Rundunar sojin kasar ta bayyana kwace Yabrud a matsayin wata babar nasara wajen karbe iyakar kasar Lebanon, da kuma katse hanyar da ake kaiwa Yan Tawayen makamai.

Garin na Yabrud mai dauke da mutane Dubu 30 cikin su har da kiristoci na daya daga cikin yankunan da ‘Yan tawaye suka kwace a baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.