Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Majalisar dunkin Duniya ta bukaci Iran ta sa Baki a sasanta rikicin Sirya

Jakadan Majalisar dinkin Duniya da ke shiga tsakani a rikicin kasar Siriya Lakhdar Brahimi, ya isa kasar Iran dan ganawa da hukumomin kasar, domin ganin sun sanya hannu dan magance matsalar kasar Siriya

Iran
Iran rfi.fr
Talla

Ana saran Brahimi zai gana da shugaba Hassan Rouhani da ministan harkokin wajen kasar, Mohammed Javad Zarif a ziyarar tashi ta kwanaki Uku.

Kasar Iran na daya daga cikin kasashen da ke fada aji a kasar Syria, kuma itace kasar Amurka da Israela, a dayan bangaren kuma da ‘yan tawayen Siriya masu samun taimakon kassahen yammaci, suka nunawa rashin amincewa da halartar taron tattaunawar da dama da aka kira a baya.

Sai dai abin ban mamakin a yau shi ne yanda Majalisar dunkin Duniya da kanta, ta bukaci Iran ta saka Baki domin warware rikicin kasar Siriyar da ya ki ci ya ki cinyewa.

Yanzu haka dai an shiga Shekara ta 4 da ake tafka fada tsakanin Sojin Gwamnatin shugaba Assada da na ‘yan tawayen kasar masu samun tallafin Turawan yammacin Duniya domin kifar da Gwamnatin kasarsu.

A baya dai sai da Amurka da sauran kasashen Yamma suka bada sanarwar katsiye baiwa ‘yan tawayen tallafi lura da yanda suka dan kasawa ayyukan da suka saka su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.