Isa ga babban shafi
Korea

Shugabannin Korea sun yi ganawa mai cike da tarihi

Bayan ganawar tarihi tun da sanyin safiyar yau juma’a kusa da iyakokin kasashen biyu, shugabannin Korea ta Arewa da Korea ta Kudu sun gudanar liyafar cin abincin rana a tare. Shugabannin biyu dai na wannan ganawa ce tare da rakiyar ministoci da kuma manyan hafsoshin sojin kasashensu.

Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un da takwaransa na Korea ta Kudu Moon Jae-in
Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un da takwaransa na Korea ta Kudu Moon Jae-in Host Broadcaster via REUTERS TV
Talla

Wannan dai shi ne karo na uku a cikin shekaru 65 da shugabannin kasashen biyu da ba sa ga maciji  ke ganawa da juna da nufin warware tsohuwar kiyayyar da ke tsakaninsu, wadda ta samo asali daga bambancin ra’ayi na siyasa.

Kafafen yada labaran kasashen biyu sun nuna hoton shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un a cikin bakaken tufafi na takawa da kafa domin tsallaka layin da ya raba kasashen biyu, a daidai lokacin da takwaransa Moon Jae-in ke jiran sa a daya bangaren, in da nan take suka yi musafaha tare da alamar murmushi a fuskokinsu.

Daga nan ne kuma shugabannin biyu suka yi tsit tare da fuskantar wasu jami’an tsaro na musamman da ke sanye da tufafi da kuma kida irin na gargajiya na musamman da aka tsara domin wannan ganawa.

Kafin wannan ganawa, shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in, ya ce yana da kwarin gwiwar za a kulla wata muhimmiyar yarjejeniya tsakanin kasashen biyu, yayin da takwaransa Kim Jong-un ke cewa a shirye yake ya ziyarci birnin Seoul a duk lokacin da ya samu goron gayyata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.