Isa ga babban shafi
FAO

Mutane miliyan 820 na fama da yunwa a duniya

Yau ita ce ranar abinci ta duniya, wadda ta yi daidai da ranar da aka kafa Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya wato FAO. Sai dai ranar ta bana na zuwa ne a daidai lokacin da miliyoyin mutane ke fama da yunwa.

Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kara kaimi wajen noman abinci mai gina jiki
Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kara kaimi wajen noman abinci mai gina jiki Laurent Correau / RFI
Talla

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, yanzu haka akwai mutane kimamin miliyan 820 da ke fama da yunwa ko kuma rashin abinci mai gina jiki a sassan duniya.

Hukumar FAO ta bukaci jama’a da su rika cin abinci mai gina jiki da suka hada da ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki tare da kaurace wa na’ukan cimaka masu haifar da taiba.

Hukumar ta FAO ta ce, mutane na fama da kibar da ta wuce kima saboda dabi’arsu ta kaurace wa na’ukan abincin gona masu gina jiki, inda suka rungumi abinci mai kitse da sikari da gishiri, sannan kuma suke yawan cin naman shanu.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa, akwai mutane miliyan 670 da ke fama kibar da ta wuce kima baya ga kananan yara miliyan 160 da su ma ke fama da irin matsalar saboda rashin daidaiton cimaka.

FAO ta bayyana cewa, dungulewar duniya wuri guda, da gina manyan birane da kuma habbakar kudaden shiga, su ne ummul-haba’isin kasalar da ke hana mutane ware lokacin girki a gida, in da a maimakon haka suke sayen abincin da ke illa ga lafiyarsu a manyan shaguna.

A bangare guda, Hukumar ta ce, al’ummar duniya na fuskantar matsalar karancin abinci, abin da ke hana su samun isassun abinci masu kara lafiya ga jiki.

Kwararru a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa, rashin abinci mai gina jiki na haifar da cututtuka da dama ga bil’adama, kuma akwai bukatar hada karfi da karfe wajen magance wannan matsalar a cewar FAO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.