Isa ga babban shafi
Gambiya

An Sami Manyan Sojan Da Laifi

Masu gabatar da kara a kasar Gambia,  yau sun gurfanar da tsohon Hafsan Sojan ruwan kasar da kuma tsohon Hafsan Sojan kasa na  kasar, saboda samunsu da hannu wajen  yunkurin kifar da Gwamnatin Shugaba Yahya Jammeh cikin watan uku na 2006.A yau ne ake sa ran Tsohon Hafsan Sojan Ruwan, Sarjo Fofona da tsohon Hafsan Sojan kasa na kasar Langtombong Tamba zasu gurfana gaban kotu a birnin Banjul.Kamar yadda mai gabatar da kara ya bayyana mutanen biyu na sane da yunkurin juyin mulki amma kuma sukayi kememe suka ki tona asirin yunkurin ga mahukunta.Ya zuwa yanzu dai akwai mutane akalla 11 dake gidan sarka saboda zargin yunkurin kifar da Gwamnatin Yahya Jammeh cikin shekara ta 2006.Suna zaman gidar yarin ne na tsawon shekaru 20 zuwa waadin zaman rai da rai.Shi kansa Shugaba Yahya Jammeh, a shekara ta 1994 ya hau kujeran mulkin kasar bayan ya kifar da Gwamnati. 

rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.