Isa ga babban shafi
Gambia

Tsohon Jakadan Gambia dake Faransa Ya Gurfana Gaban Kotu

Wani tsohon Jakadan kasar Gambia a kasar Faransa William John Joof yau wata kotu ta zarge shi da laifin cin hanci da sata a lokacin da yake ofis.Da ake sauraron karar yau a Banjul tsohon Jakadan wanda yanzu yake rike da mukamin Babban Sakatare na Ma'aikatar Harkokin Waje na kasar, ya karyata zargin da akeyi masa.Kotun taki bada belin sa, kuma za'a cigaba da tsare shi a gidan yari.John Joof ya rike Jakadan kasar Gambiya  a kasar Faransa tsakanin shekara ta 2002 zuwa shekara ta 2007.Ana tuhumar sa ne da laifuka tara, da suka hada da mallakan wasu kayayyaki ta haramtacciyar hanya, yiwa gwamnati zagon kasa da karya dokokin aikin Gwamnati.Bayanan na nuna cewa tsohon Jakadan yayi amfani da sunansa wajen shiga kasar da wasu kayayyaki gudun kada a karbi kudaden fito daga hannun masu su da kuma karban kudaden Turai Euro 15,000 daga wani dan kasar Faransa domin ya bashi aiki a ofishin jakadanci.  

Shugaban Gambiya Yahya Jammeh
Shugaban Gambiya Yahya Jammeh rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.