Isa ga babban shafi
Najeriya

MEND ta dauki alhakin garkuwa da Ma’aikata

A yau Talata, tsagerun Niger Delta sun bada sanarwar daukar alhakin kai harin ranar lahadi, inda suka yi garkuwa da ma’aikata masu hako mai guda biyar a kauyen Okoro da ke Jahar Akwa Ibom.a kwanan baya ne kungiyar ta MEND ta aika da gargadin kai sabbin hare hare a wasu daga cikin bututun man kasar.Wannan harin dai ya faru ne a jiya lahadi kauyen Okoro da ke karamar hukumar Obolo Jahar Akwa Ibom.Bayanan da ke fitowa daga jami’an tsaron kasar, an bayyana cewa, ma’aikata biyu daga cikin wadanda aka yi garkuwa dasu ‘yan kasar Faransa ne biyu kuma ‘yan kasar Amurka, daya kuma dan kasar Canada.A ranar talatan da ta gabata ne kungiyar MEND ta bada sanarwar zata kai wasu sabbin hare hare a makonni masu zuwa. Kuma a sakon da ta aika ta hanyar Email kungiyar ta bayyana cewa a yanzu haka tana rike da wasu ‘yan kasar waje guda hudu wadanda ta yi garkuwa dasu makwannin biyu da suka gabata, da suka hada da dan kasar Thailand daya da kuma wasu mutane uku ‘yan kasar Faransa.Wannan aikin ta’addancin a yankin Niger Delta, wani kalubale ne dai ga shugaba Goodluck Jonathan, wanda shi ne shugaba na farko da ya fito daga yankin Niger Delta, wanda kuma a yanzu haka ke fuskantar kalubale tsakanin shi da ‘yan arewacin kasar a zaben kasar da za’a gudanar watan Aprilun shekara mai zuwa. 

Tsagerun Mend Masu yakin neman 'yancin Niger Delta
Tsagerun Mend Masu yakin neman 'yancin Niger Delta guerre totale
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.