Isa ga babban shafi
Najeriya

MEND ta dauki alhakin kai harin Exxon

A yau talata Kungiyar MEND mai fafutikar neman ‘yancin yankin Niger Delta ta fito ta bayyana daukar alhakin kai harin kamfanin Man fetir na Exxon Mobil, inda kungiyar ta yi garkuwa da ma’aikatan kamfanin guda bakwai.A wani sako da kungiyar Ta MEND ta aikawa manema labarai, kungiyar ta bayyana cewa nan bada jimawa ba ne zata kaddamar da sabbin hare hare ga kamfanonin man Fetir da ke yankin Niger Delta.Kamfanin da ke hako mai a Jahar Akwa Ibom da ke a yankin Niger Delta da Allah ya albarkata da man Fetir a Najeriya, wannan harin shi ne na biyu da ake kaiwa a mako daya a wannan yankin.A makon jiya ne dai aka kaiwa kamfanin hako Man Fetir na Afren hari, inda aka yi garkuwa da ma’aikatan kamfanin da suka hada da Amurkawa biyu da faransawa biyu da kuma ‘yan kasar Indonisiya biyu da dan kasar Canada mutum daya. Harin da kuma Kungiyar MEND mai fafutikar yakin neman ‘yancin Niger Delta ta yi ikirarin daukar alhaki tare da gargadin sake kai wasu hare haren a wannan yankin. 

Tambarin kamfanin Exxon Mobil
Tambarin kamfanin Exxon Mobil (Photo : RFI)
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.