Isa ga babban shafi
Liberia

Sirleaf a Liberiya ta zabi Ministoci

Shugabar kasar Liberiya Allen Sirleaf ta zabi sabbin Ministoci biyar a yau Alhamis bayan da ta sauke ministocin makwannin uku da suka gabata.A sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasar, shugabar ta zabi minista mai kula da hararkar Noma da Ministan tsare tsare da kuma tattalin arziki, sai kuma Ministan shari’a da Ministan wasanni da kuma Ministan Ayyuka.A yanzu haka an rantsar da Ministocin inda suka amince da mukamin da aka basu tare da alkawalin aiki tukuru da shugabar don cigaban al’ummar kasar.4 ga watan Nuwamba ne shugaba Sirleaf dake neman sake tsayawa takara a zaben kasar da za’a gudanar shekarar 2011 ta dakatar da Ministocinta. 

Shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf lokacin da ta ziyarci taron kasashen larabawa a Africa
Shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf lokacin da ta ziyarci taron kasashen larabawa a Africa Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.