Isa ga babban shafi
Cote d’ivoire

Akwai ci gaba a ziyarata kasar Cote d’Ivoire, inji Obasanjo

A ziyarar kwana daya da Tsohon shugaban kasar Najeriya Cip Olusegun Obasanjo ya kai kasar Cote d’Ivoire domin sasanta rikicin siyasar kasar, tsohon shugaban ya ce yana da kwarin gwiwa wajen shawo kan rikicin kasar cikin ruwan sanyi ba tare da amfani da karfin soji ba don tumbuke Laurent Gbagbo daga kujerar shugabancin kasar.Mista Gbagbo dai ya tirje duk da matsin lambar da kungiyoin kasashen duniya ke masa na sai ya sauka daga kujerar shugabancin kasar bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Nuwamba bara, inda duniya ta amince da abokin hamayyarsa Alassane Ouattara a matsayin shugaban da ya lashe zaben.Tuni dai kasashen duniya suka kakubawa Laurent Gbagbo takunkumi tare da makaranbansa amma duk da haka shugaban ya bijerewa matakan na lalama da aka bi kan sai ya sauka daga kujerar shugabancin kasar domin goyon bayan sojin kasar da ya samu.A ranar Assabar din da ta gabata ne Cip Olusegun Obasanjo ya kai wata ziyarar ba zata a wani yunkuri na shawo kan Gbagbo ya mika mulki cikin lumana da kwanciyar hankali.Lokacin da tsohon shugaban ya ke ganawa da manema labarai, a masaukinsa wata Otel a Abidjan babban birnin kasar, Obasanjo yace ziyararsa zata taimaka matuka.Shugaban ya kwashe awanni a jiya lahadi yana ganawa da Gbagbo da Alassane Ouattara domin shawo kan rikicin siyasar kasar da ya-ki ci ya-ki cinyewa. Karo biyu kungiyar ECOWAS na kokarin tattaunawa da Gbagbo karkashin jagorancin Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan domin shawo kan rikicin kasar amma hakan ya faskara. A yanzu haka dai kunkiyar ta yi gargadin amfani da karfin Soji domin fitar da Gbagbo daga kujerar shugabancin kasar. 

Tsohon Shugaban Najeriya Cip Olusegun Obasanjo
Tsohon Shugaban Najeriya Cip Olusegun Obasanjo (Photo : AFP)
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.