Isa ga babban shafi
Najeriya

MEND ta yi gargadin kai hari a matatun Man Fetir a Najeriya

A yau talata kungiyar MEND mai fafutikar neman ‘yancin Niger Delta a tarayyar Najeriya ta yi gargadin kai wasu sabbin hare hare ga matatun man petir din kasar a wani sako da kungiyar ta yada da ke nuna adawa da gwamnati kan cafke wasu daga cikin ‘yayanta.Sakon wanda ke dauke da sanarwar cewa: “kungiyar MEND zata kaddamar da sabbin hare hare ga matatun man fetir din Najeriya, kuma muna kira al’ummar kasar mazauna kusa da matatun man da su kaura don kaucewa rasa rayuka”.Ba tare da bayyana asalin ‘yayan kungiyar da gwamnatin kasar ta cafke ba, kungiyar tace ba zata zura ido ba gwamnati na karya su ba tare da aikata laifi ba.Kungiyar MEND dai ita ce ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin Abuja babban birnin kasar lokacin da kasar ke bukin cika shekaru hamsin na samun ‘yan cin kai.Wannan sanarwar dai na zuwa ne a daidai lokacin da Charles Okah daya daga cikin shuwagabannin kungiyar zai gurfana gaban kotu wanda ake zargin kai harin 1 ga watan Octoban bara kodayake an samu jinkiri a zaman kotun bayan ya suma a harabar kotun.Shekarun baya kungiyar MEND ta sha kai hare hare tare da garkuwa da ma’aikatan kamfononin Man Fetir a yankin Niger Delta. 

'Yan tawayen yankin Niger Delta
'Yan tawayen yankin Niger Delta guerre totale
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.