Isa ga babban shafi
Uganda

‘Yan sandan Uganda sun harbi madugun adawa ga hannu

A yau Alhamis ‘yan sandan kasar Uganda sun harbi Madagun adawar kasar Uganda Kizza Besigye ga hannu lokacin da suke kokarin haramta masa gudanar da zanga-zanga da shi da magoya bayansa. Patrick Wakidi na hannun damar Kizza Besigye ya bayyanawa manema labarai cewa ‘yan sandan Uganda sun harbe shi ne da wani albarushi kirar roba, anan take ne kuma suka dauke shi zuwa asibiti.Kungiyar Agaji ta Red Cross ta tabbatar da cewa Kizza Besigye ya samu rauni sosai. Kungiyar ta tabbatar da cewa mutane kimanin 30 ne yanzu haka ke kwance a gadon asibiti sanadiyar arangama da ‘yan sanda.Kizza Besigye ya shirya gudanar da zanga-zangar ne domin kalubalantar shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni bayan bayyana shugaban a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka gudanar. 

Kizza Besigye madugun adawar kasar Uganda lokacin da yake yakin neman zabe.
Kizza Besigye madugun adawar kasar Uganda lokacin da yake yakin neman zabe. the equatorian
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.