MDD-Libya
MDD tace zata taimakawa zaben Libya
Majalisar Dunkin Duniya tace a shirye ta ke ta taimakawa gwamnatin ‘Yan Tawayen Libya a shirye shiryensu na gudanar da zabe a cikin kasar.A cewar Jekadan Majalisar Dunkin Duniya a Tripoli Ian Martin, a jerin bukatun da ‘Yan Tawayen suka fi ba muhimmaci domin tallafa masu shi ne shirya gudanar da zabe.Tun a karshen mako nan ne jekadan Majalisar Dunkin Duniya mai bai wa Ban Ki-moon Shawara ya kai ziyara a Tripoli domin tattaunawa da hukumomin Libya dangane da hanyoyin da suke Tunanin Majalisar Dunkin Duniya zata taimaka masu.
Wallafawa ranar: