Isa ga babban shafi
Libya

PM na Turkiyya Erdogan ya ziyarci kasar Libya

Mayakan dake fafatawa domin tabbatar da sabuwar Gwamnatin rikon kwarya akasar Libya ta zauna, na can suna cigaba da barin wuta a yankin garin Sirte da kuma Bani Walid, garuruwa da suka rage da ake ganin Hambararren Shugaban kasar Moammar Gaddafi na da karfi.A waje daya kuma PM kasar Turkiyya Recep Tayip Erdogan na ziyara yau a birnin Tripoli inda yace yana wannan ziyara ce domin karfafa dankon zumunci.Yace abin farin ciki ne yadda ya shaida samun ‘yancin kasar Libya. Yace yana wannan ziyara saboda kara nuna irin zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.  

Shugaban Gwamnatin Riko ta Libya, Mustafa Abdel Jalil
Shugaban Gwamnatin Riko ta Libya, Mustafa Abdel Jalil REUTERS/Esam Al-Fetori
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.