Isa ga babban shafi
Libya

Jibril yace zai yi Murabus bayan tabbatar da ‘yancin Libya

Prime Ministan rikon kwaryar gwamnatin Libya yace zai yi murabus idan har ‘Yan Tawaye suka karbe ikon birnin Sirte Mahaifar Gaddafi.Sanarwar ta Jalil na zuwa ne bayan yunkurin sauya Majalisar Ministocin gwamnatin ‘yan Tawayen.Tun bayan karbe ikon birnin Tripoli ne Gwamnatin ‘Yan tawayen ta bayyana kafa sabuwar gwamnatin da zata wakilci jama’ar kasar.An dai fara samun sabani tsakanin ‘Yan tawayen inda mafi yawancinsu suka bukaci Salem Joha kwamandan soji daga Misrata ya karbi mukamin Ministan tsaro amma kuma shugaban ‘Yan Tawayen Mustafa Abdul Jalil ya bada sanarwar cewa Jalal Dghaili ne zai ci gaba da tafiyar da sha’anin tsaron domin kimar sa ga idon al’ummar muslmin kasarKwarya-kwaryar kundin tsarin mulkin kasar na ‘Yan Tawayen ya tsara cewa cikin shekara daya ne za’a gudanar da zaben ‘yan Majalisu da zaben shugaban kasa.Kuma kundin tsarin mulkin kasar ya haramtawa Mambobin gwamnatin ‘Yan tawayen tsayawa takarar zabe bayan kifar da gwamnatin Gaddafi 

Shugaban NTC Mustapha Abdeljalil,
Shugaban NTC Mustapha Abdeljalil, Reuters/Kevin Lamarque
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.