Isa ga babban shafi
Liberiya

Zaben Shugaban kasar Laberiya

A yau Talata ne ake gudanar da zaben shugaban kasa karo na biyu a kasar Liberiya tun bayan yakin basasa. Inda kasashen Duniya ke neman ganin an gudanar da zaben ba tare da wani tashin hankali ba a cikin kasar.Za’a gudanar da zaben ne tsakanin shugabar kasar Ellen Johnson-Sirleaf, da ‘yan takara 15 cikinsu har da tsohon jami’in Majalisar Dunkin Duniya Winston Tubman wanda shahararren dan wasan kwallon kafar kasar Goerge Weah ke take ma baya a matsayin Mataimaki.Al’ummar kasar Liberiya dai na fama da matsalar rashin aikin yi, inda daruruwan mutane ke bara akan tituna da suka samu rauni a lokacin yakin basasa. ‘Yan kasar na zama ne kasa da Dala 1 a rana. 

Jerin masu jiran kada kuri'a a zaben shugaban kasa a Liberia
Jerin masu jiran kada kuri'a a zaben shugaban kasa a Liberia REUTERS/Luc Gnago
Talla

00:23

Farfesa Umar Fate na Jami'ar Maiduguri a Najeriya

Da farko Johnson-Sirleaf ta yi watsi da tazarce, daga bisani ta canza shawara inda ta bayyana bukatar sake wa’adi na biyu domin magance matsalolin kasar.

Taken yakin neman zabenta shi ne “Biri na aiki, Biri ka kara hakuri” ‘Yan kasar Liberiya su kara hakuri.

Zaben Shugaban kasar shi ne irinsa na farko da kasar zata shirya da kanta tun bayan kawo karshen yaki a shekarar 1989 zuwa 2003, rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan rabin Miliyan.

Johnson-Sirleaf ita ce mace ta farko a matsayin shugabar kasa a Africa bayan zabenta a zaben da Majalisar Dunkin Duniya ta gudanar a shekarar 2005.

Masu saka ido a zaben suna ganin Tubman na Jam’iyyar CDC da mataimakinsa George Weah zasu taka rawar gani a zaben inda ake hasashen zasu kalubalanci Johnson-Sirleaf a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.