Isa ga babban shafi
SUDAN

An cafke madugun adawa a Sudan

Nahla ‘Yar madugun adawa Faruk Abu Isah ta shaidawa kamfanin dillacin labaran Reuters cewa jami’an tsaro a kasar Sudan sun cafke mahaifinta a gidansa da ke birnin Khartoum.“Ba mu san dalilin kama shi ba, kuma bamu san inda aka tafi da shi ba, baya cikin koshin lafiyar da za’a kama shi domin yana fama da ciwon hawan jini” inji Nahla.A cewar kafar yada labaran Sudan ta SMC, Abu Issa ya bukaci ofishin jekadancin kasar Holland ya tallafa masa da kudi domin hada wani kazamin gangami domin hambarar da Shugaba Umar Hassan Al Bashir.Abu Issa shi ne shugaban kawancen Jam’iyyun adawa, kuma ya dade yana buya a kasar Masar kafin dawowarsa a shekarar 2005 da gwamnati ta nemi sasantawa da ‘yan Adawa.Har yanzu dai jami’an tsaro basu ce komi akan cafke Abu Issa. 

Madugun Adawa a Sudan Farouk Abu Issa
Madugun Adawa a Sudan Farouk Abu Issa @Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.