Shugabannin Duniya suna ganin karshen Gaddafi shi ne karshen Mulkin kama-karya
Shugabannin kasashen duniya sun yi jinjina ga mutuwar tsohon shugaban Libya Muammar Gaddafi, tare da danganta karshensa a matsayin karshen mulkin kama-karya tare da fatar ganin gina sabuwar kasar Libya.Bayan sanar da mutuwar Gaddafi Shugaban kasar Amurka Barrack Obama yace mutuwar shugaban ita ce karshen babin bakin-ciki a kasar Libya, tare da kiran hada kan ‘yan tawaye wajen kokarin gina sabuwar Libya.
Wallafawa ranar:
Rehoton cafke Gaddafi
Fira Ministan Birtaniya David Cameron yace mutuwar Gaddafi wata dama ce wajen girka Demokradiyya a Libya bayan bayyana wadanda suka mutu karkashin tsohon shugaban tun a harin Lockerbie a shekarar 1988.
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy yace al’ummar Libya sun yi yakin neman ‘yanci daga gwamnatin danniya bayan kwashe shekaru 40 tana mulkinsu.
Martanin Shugabannin kasashen Duniya
Faransa da Amurka da Birtaniya sune kasashen da suka jagoranci yaki a libya ta mafani da NATO da suka kaddamar da hare hare kusan 1,000 tun a watan Mayu.
Kasar China da ke adawa da NATO ta yi fatar ganin an girka sabuwar Libya cikin lokaci kalilan domin kare al’umma da ci gabansu.
Tarihin Gaddafi
Sai dai kuma Shugaban Venuzeula Hugo Chavez yace kisan Gaddafi kisan gilla ne, a cewarsa zasu ci gaba da tuna Gaddafi a matsayin jarumi wanda ya mutu da kishin kasarsa.
A kasar Itali da ta mulki kasar Libya, Fira Ministan kasar Silvio Berlusconi yace yanzu yaki ya kawo karshe tare da fatar zaman lafiya a Libya bayan kawo karshen Gaddafi
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu